Dattijon Arewa Ya Yi Kira Ga Hukumomi Kan Lamarin El-Rufai



Ibrahim sahabi 

Daya daga cikin dattawan Arewa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya yi kira ga hukumomin da ke rike da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da su tabbatar da bin doka a kan lamarin da ya shafe shi.

Ya ce idan har ana zarginsa da wani laifi, ya kamata hukumomi su fito su bayyana hujjojin da ke tabbatar da zargin a fili.

A cewarsa, a kasa mai bin dimokuradiyya ba daidai ba ne a rike mutum ba tare da bayyana laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

Ya kara da cewa ko mutum yana goyon bayan siyasar El-Rufai ko baya goyon bayanta, dole ne a tabbatar an bi doka.

Dr. Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya jaddada muhimmancin adalci da gaskiya.

Comments

Popular posts from this blog

ABUTH Zaria inducts 267 Health Information technicians, technologists

Usman Sulaiman emerges ASUP NBPZ Chairman unopposed, pledges inclusive leadership

MBY Declares Intention to Contest for Zaria Federal Constituency Seat in 2027