FASHEWAR BOM A KWARA: Direba Ya Mutu, Uwa Ta Jikkata, Jariri Ya Tsira Lafiya


Wani fashewa da aka danganta da bam din hannu (IED) da ake zargin ‘yan bindiga ne suka dasa ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da jikkata wata mata a kauyen Woro da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara. Lamarin ya faru ne da safiyar yau, inda rahotanni suka tabbatar da cewa wani direban mota ya rasa ransa a wurin.


Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Adekimi Ojo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya karyata rahotannin da ke cewa mutane da dama sun mutu. Ya bayyana cewa fashewar ta shafi direban mota, wata fasinja mace, da kuma uwa mai shayarwa da jaririnta.

A cewarsa, direban ya mutu nan take bayan ya taka bam din, yayin da matar ta samu munanan raunuka. Sai dai jaririn da take dauke da shi bai samu ko daya daga cikin raunukan ba, lamarin da ya bai wa mutane mamaki da godiya ga Allah.

Wani mazaunin yankin, Dakta Abdul Woro, ya ce an dasa bam din ne a bakin hanya, kuma ya fashe ne da zarar motar ta wuce. Shugaban karamar hukumar Kaiama, Honarabul Abubakar Abdullahi, ya bayyana cewa harin na da alaka da ramuwar gayya daga ‘yan bindiga bayan kama wasu daga cikinsu da kuma dakile hanyoyin da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa an samu bam guda biyu amma daya ne kawai ya fashe. Ya ce jami’an tsaro sun riga sun shawo kan lamarin tare da kara tsaurara tsaro a yankin domin hana sake faruwar irin wannan hari, tare da kira ga al’umma da su rika bayar da hadin kai wajen gano masu taimakawa ‘yan bindiga.

Comments

Popular posts from this blog

ABUTH Zaria inducts 267 Health Information technicians, technologists

Usman Sulaiman emerges ASUP NBPZ Chairman unopposed, pledges inclusive leadership

MBY Declares Intention to Contest for Zaria Federal Constituency Seat in 2027