“Fifita Yanki, Kabilanci da Addini Sama da Hadin Kan Kasa Na Haddasa Matsalolin Najeriya”


Fitacciyar mai amfani da shafukan sada zumunta, Amina Isiyaku, ta bayyana cewa wahalhalun da ake fuskanta a Najeriya na ci gaba ne saboda abin da ta kira tsaurara ra'ayi a bangaren addini, bangarencii da kabilanci.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, Amina Isiyaku ta ce matsalolin kasar ba wai kawai sakamakon shugabanci ba ne, har ma da yadda wasu ‘yan kasa ke fifita addini, yanki da kabila fiye da hadin kan kasa.

Ta kara da cewa idan ‘yan Najeriya ba su daina kallon al’amura ta fuskar addini, yanki ko kabila ba, wahalhalun kasar za su ci gaba. Ta jaddada cewa ci gaban kasa na bukatar hadin kai da fahimtar juna.

Sakon nata ya haifar da muhawara a tsakanin masu bibiyarta a shafukan sada zumunta, inda wasu suka goyi bayan ra’ayinta, yayin da wasu kuma suka soki kalaman nata. Duk da haka, batun ya sake tayar da tattaunawa kan rarrabuwar kawuna a Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

ABUTH Zaria inducts 267 Health Information technicians, technologists

Usman Sulaiman emerges ASUP NBPZ Chairman unopposed, pledges inclusive leadership

MBY Declares Intention to Contest for Zaria Federal Constituency Seat in 2027