Gwamna Yusuf ya yaba da dangantakar Najeriya da Saudiyya

Kano – 9 ga Maris, 2026

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada ƙaƙƙarfan dangantaka da ke tsakanin Najeriya da Masarautar Saudiyya, yana mai cewa dangantakar ta ginu ne a kan tarihi mai zurfi, addini da kuma hulɗar tattalin arziki da suka daɗe suna ƙarfafa juna.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Babban Sakatarensa na Musamman, Dr. Sulaiman Wali Sani, a ranar Lahadi a Kano yayin wani taron buɗa-baki (Iftar) da Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Kano ya shirya a cikin watan Ramadan.

Ya ce dangantakar ƙasashen biyu ta daɗe tana ƙara ƙarfi sakamakon alaƙar al’adu da addini, musamman tsakanin Jihar Kano da Saudiyya. Ya ƙara da cewa Kano ta dade tana cin gajiyar haɗin gwiwa da Saudiyya a fannoni kamar addini, ilimi, kasuwanci da kuma ayyukan raya ƙasa.

A cewarsa, Najeriya da Saudiyya na ci gaba da haɗa kai wajen aiwatar da shirye-shiryen tattalin arziki da ayyukan jin ƙai da nufin inganta rayuwar al’umma.

Gwamna Yusuf ya kuma kawo misalin gudummawar tsiron dabino guda 1,000 da Saudiyya ta bayar domin dasawa a jihar, yana mai cewa shirin zai taimaka wajen kare muhalli, inganta abinci da kuma ƙara bunƙasa tattalin arziki.

Ya tabbatar wa gwamnatin Saudiyya cewa Jihar Kano za ta ci gaba da ƙarfafa dangantakarta da masarautar, tare da gode wa ofishin jakadancin Saudiyya kan shirya taron buɗa-bakin.

Shi ma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, wanda ya halarci taron, ya ce duk da cewa Kano ce ke karɓar ofishin jakadancin Saudiyya, Jihar Jigawa ma tana cin gajiyar kyakkyawar dangantakar da tallafin masarautar.

Ya yabawa ofishin jakadancin Saudiyya bisa karamci da kulawa da yake nunawa, musamman wajen shirya taron buɗa-baki na shekara-shekara da ke haɗa shugabanni da masu ruwa da tsaki.

A nasa jawabin maraba, Jakadan Saudiyya a Kano, Khalil bin Ahmed bin Ali Adamawi, ya gode wa manyan baƙi da suka halarci taron, yana mai cewa irin wannan taro na nuna ruhin watan Ramadan wanda ke ƙarfafa haɗin kai, tausayi da kuma ƙara dankon zumunci tsakanin al’umma.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati daga jihohin Kano da Jigawa, jami’an diflomasiyya, malamai (Ulama), shugabannin hukumomin tsaro da na paramilitary, da kuma wakilan ‘yan kasuwa.

Comments

Popular posts from this blog

ABUTH Zaria inducts 267 Health Information technicians, technologists

Usman Sulaiman emerges ASUP NBPZ Chairman unopposed, pledges inclusive leadership

MBY Declares Intention to Contest for Zaria Federal Constituency Seat in 2027