Gwamnatin Najeriya Ta San Duk ‘Yan Ta’adda da inda suke.



Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta san yawancin ‘yan ta’adda da sunayensu da kuma wuraren da suke.

Malamin ya ce duk lokacin da ake kokarin tattaunawa da su, ba ya yin hakan shi kadai, domin yana yin hakan ne tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na gwamnati.

A cewarsa, hukumomin tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji da sauran hukumomi na sane da duk wani mataki da ake dauka a irin wadannan tattaunawa.

Sheikh Gumi ya kara da cewa manufarsa a irin wannan lamari ita ce kokarin samar da zaman lafiya da kuma rage tashin hankali tsakanin bangarorin da ke rikici.

Ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da tashar DRTV Nigeria ta wallafa, inda ya yi karin bayani kan rawar da yake takawa wajen tattaunawa da wasu daga cikin ‘yan bindiga.

Comments

Popular posts from this blog

ABUTH Zaria inducts 267 Health Information technicians, technologists

Usman Sulaiman emerges ASUP NBPZ Chairman unopposed, pledges inclusive leadership

MBY Declares Intention to Contest for Zaria Federal Constituency Seat in 2027