Gwamnatin Najeriya za ta samar da wutar sola a asibitoci 371 don inganta kiwon lafiya.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da wani shiri na samar da tsayayyar wutar lantarki ta hanyar sola a asibitocin matakin farko (PHCs) guda 371 da ke jihohi 16 na Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja. An ce shirin na da nufin inganta ayyukan kula da marasa lafiya musamman wajen gudanar da allurar rigakafi da kula da lafiyar mata masu juna biyu.

An kaddamar da shirin ne a wani taro da Hukumar Bunƙasa Asibitoci a Matakin Farko (NPHCDA) ta shirya a Abuja. Babban Daraktan hukumar, Muyi Aina, ya bayyana cewa samar da wutar sola zai taimaka wajen ba da tsayayyar wutar lantarki ga asibitocin da ke fama da matsalar rashin wuta, domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A cewarsa, tsayayyar wutar lantarki na da muhimmanci wajen adana allurar rigakafi da kuma gudanar da ayyukan ceton rayuka kamar kula da mata masu juna biyu da masu neman agajin gaggawa. Ya kara da cewa wutar lantarki ba abin jin dadi ba ne kawai, illa wajibi ne ga asibitoci domin gudanar da ayyukan lafiya cikin inganci.

Hakazalika, babbar jami’ar Gavi, Sania Nishtar, ta ce cibiyarsu ta zuba jarin sama da dala biliyan 2.4 a shirin allurar rigakafi a Najeriya cikin shekaru biyu da suka gabata. Ta ce hadin gwiwar ya taimaka wajen kara yawan yaran da ke samun allurar rigakafi daga kashi 27 cikin dari a shekarar 2001 zuwa kashi 67 cikin dari a shekarar 2024.

Ita ma wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed Abdelatef, ta yaba da kokarin Najeriya wajen karfafa asibitoci a matakin farko. Ta ce samar da tsayayyar wutar lantarki a cibiyoyin lafiya zai taimaka wajen inganta ayyukan allurar rigakafi, kula da mata masu juna biyu da kuma rage gibin samun ingantaccen kulawar lafiya a tsakanin al’umma.

Comments

Popular posts from this blog

ABUTH Zaria inducts 267 Health Information technicians, technologists

Usman Sulaiman emerges ASUP NBPZ Chairman unopposed, pledges inclusive leadership

MBY Declares Intention to Contest for Zaria Federal Constituency Seat in 2027