Matasan Najeriya su tashi tsaye don tabbatar da ingantaccen shugabanci — Ahmad Aminu Vertical
Daga Wakilinmu.
An bukaci matasan Najeriya da su tashi tsaye domin tabbatar da ingantaccen shugabanci a matakai daban-daban a fadin kasar nan. Wannan kira ya fito ne daga fitaccen matashin dan siyasa, Hon. Engr. Ahmad Aminu Vertical, yayin da yake tattaunawa da wakilin jaridar FRONTLINE Report cikin sakon barka da Sallah da ya aike wa al’ummar karamar hukumar Sabon Gari.
Ahmad Aminu Vertical ya bayyana cewa lokaci ya yi da matasa za su dauki nauyin gina makomarsu ta hanyar shiga harkokin shugabanci da bayar da gudunmawa mai ma’ana a fannoni daban-daban. Ya ce matasa su ne ginshikin ci gaban kowace kasa, don haka dole ne su zama masu taka rawa wajen samar da shugabanci nagari.
Ya kara da cewa a halin yanzu babu abin da matasa ke bukata sama da ingantaccen ilimi, bunkasa kimiyya da fasaha, da kuma samar da ayyukan yi. A cewarsa, wadannan su ne muhimman abubuwan da za su taimaka wajen ciyar da kasa gaba da rage matsalolin rashin aikin yi da talauci.
Ya jaddada cewa matasa su kansu ne suka fi dacewa su jagoranci kansu wajen cimma wadannan manufofi, yana mai cewa hadin kai da jajircewa na daga cikin hanyoyin da za su kai su ga nasara. Haka kuma ya bayar da misalan kasashen da suka samu gagarumin ci gaba ta hanyar bai wa matasa dama a fannoni na kimiyya, fasaha da shugabanci.
A karshe, Hon. Engr. Ahmad Aminu Vertical ya mika sakon barka da Sallah ga daukacin al’ummar musulmin duniya, tare da fatan Allah ya karbi ibadu. Haka kuma ya taya jagororin jam’iyyar ADC na tarayyar Najeriya murnar Sallah, yana mai addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba a kasa baki daya.
Comments
Post a Comment