Matatar man Dangote ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa domin sassauta wa al’ummar Najeriya
Matatar man Dangote ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa domin sassauta wa al’ummar Najeriya tasirin tsadar man fetur, a daidai lokacin da wasu ’yan kasuwa ke gargadin cewa farashin na iya zarta naira 2,000 kan kowace lita.
Wannan na zuwa ne bayan da matatar ta ƙara kusan naira 200 a kowace lita, inda farashin ya tashi daga N995 zuwa N1,175.
Rahotanni sun nuna cewa tashin farashin fetur din na da alaƙa da rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya janyo hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Bayanan kasuwa sun nuna cewa a halin yanzu kowace ganga ta ɗanyen man fetur na sayuwa tsakanin dala 110 zuwa 120.
Masana sun danganta tsadar man fetur din da toshe mashigin Hormuz da Iran ta yi, tare da hare-haren da aka kai kan wasu matatun man fetur a Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya janyo tangarɗa ga samar da man fetur a duniya.
Comments
Post a Comment