Rikicin PDP: Kotun daukaka kara ta tabbatar da dakatar da wasu kusoshin jam'iyyar
Kotun daukaka ƙara da ke zama a Abuja ta tabbatar da dakatar da tsohon Sakataren jam’iyyar PDP, Sanata Samuel Anyanwu; mai taimaka wa jam'iyyar a fannin shari'a, Kamaldeen Ajibade; Mataimakin Lauyan Jam’iyya, Okechukwu Osuoha; da Sakatare na tsare-tsare na kasa, Umaru Bature.
Kotun ta tabbatar da dakatarwar su tare da tabbatar da hukuncin da Kotun Koli ta tarayya ta yanke, wanda Alkali Justice James Omotosho ya fitar.
Haka kuma, kotun daukaka ƙara a ranar Litinin ta tabbatar da hukuncin Kotun Koli ta tarayya da aka yanke a Abuja a ranar 31 ga watan Oktoba, 2025, wanda ya dakatar da hukumar zabe mai zaman Kanta ta ƙasa (INEC) daga amincewa da sakamakon babban taron ƙasa na shekarar 2025 na jam’iyyar PDP.
Comments
Post a Comment