Shugaban Amurka, ya soki harin da Isra’ila ta kai kan babbar cibiyar makamashin gas a Iran,
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki harin da Isra’ila ta kai kan babbar cibiyar makamashin gas ta South Pars a Iran, yana mai cewa hakan bai kamata ya sake faruwa ba.
Ya bayyana cewa Amurka ba ta da hannu a harin, kuma yana zargin Isra’ila da kai farmakin ne cikin fushi sakamakon yadda rikicin Gabas ta Tsakiyar ke ƙara ƙazanta.
Trump ya kuma yi gargaɗin cewa duk wani sabon hari kan kayayyakin makamashi a Qatar zai iya haifar da martani mai tsauri daga Amurka.
Harin ya jawo ramuwar gayya a wasu wuraren makamashin gas a ƙasashen Qatar, Haɗɗaɗiyar Daular Larabawa da Saudiyya, lamarin da ke ƙara tayar da hankula a yankin.
Comments
Post a Comment