Shugaban Matasan jam'iyyar ADC a Zaria, Ya zargin gwamnatin jam'iyyar APC da rashin tabuka abin a zo a gani a kasa.
Shugaban matasan jam’iyyar ADC a karamar hukumar Zaria, Hon. Haruna Abdulkarim, ya bukaci matasa maza da mata su tashi tsaye su shiga siyasa domin kare makomar su da ta ‘yan baya. Ya ce lokaci ya yi da matasa za su taka rawa wajen kawo sauyi a cikin al’umma.
Ya bayyana cewa, gwamnatin APC a jihar Kaduna ba ta kawo wani gagarumin ci gaba ba, musamman a bangaren tsaro da ayyukan yi. A cewarsa, al’umma na kokawa kan matsalolin da suke fuskanta a kullum.
Hon. Haruna ya ce duk da haka su a jam’iyyar ADC ba su da niyyar gaba da kowa. Ya ce suna bayyana ra’ayinsu ne idan sun ga abin da bai dace ba domin kare muradun jama’ar jihar Kaduna.
Ya kara da cewa matasa da dama sun kammala karatu amma ba su da aikin yi, yayin da wasu ke bukatar tallafi domin jari ko damar karatu. Saboda haka ya bukaci su shiga ADC domin samun damar kawo ci gaba ga kansu da al’umma.
A karshe, ya bukaci matasa su yi rajista da jam’iyyar ADC a mazabunsu sannan su karbi katin membobinsu. Ya ce hakan zai taimaka wajen hada kai domin kawo sauyi a zaben shekarar 2027.
Comments
Post a Comment