“ADC Ta Samu Sabbin Shugabanni: Aliyu Lawal Ibrahim Ya Yi Alkawarin Cikakken Goyon Baya Domin Nasarar Jam’iyya”



jigo a jam’iyyar  ADC, Alhaji Aliyu Lawal Ibrahim Cairo, ya bayyana godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki bisa kammala zabukan cikin gida na jam’iyyar daga matakin gunduma, karamar hukuma da kuma jiha cikin lumana da nasara.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, Aliyu Lawal Ibrahim ya taya sababbin shugabannin jam’iyyar murna, inda ya bayyana cewa ADC jam’iyya ce mai albarka wadda ke da kyakkyawar makoma idan aka hada kai aka yi aiki tukuru domin cimma buri.

Ya kuma tabbatar da cikakken goyon bayansa ga sabbin shugabannin, yana mai cewa a shirye yake ya bayar da gudunmawar da zai iya domin saukaka ayyukansu da kuma tabbatar da nasarar jam’iyyar a zabubbuka masu zuwa daga sama har kasa.

Haka zalika, ya bukaci shugabannin da ‘yan jam’iyya da su yi amfani da damar da ke gabansu wajen hada kai da kuma bude kofa ga duk masu niyyar tallafawa jam’iyyar domin ganin ta samu rinjaye a dukkanin matakan zabe.

A karshe, ya yi addu’ar Allah ya taimaki shugabanni da al’umma, tare da fatan alheri ga Malam Ahmad Nasiru El-Rufai, jihar Kaduna, garin Zariya da kuma kasa baki daya, yana mai cewa Allah ya albarkaci jam’iyyar ADC.

Comments

Popular posts from this blog

ABUTH Zaria inducts 267 Health Information technicians, technologists

Usman Sulaiman emerges ASUP NBPZ Chairman unopposed, pledges inclusive leadership

MBY Declares Intention to Contest for Zaria Federal Constituency Seat in 2027