ADC a Zariya Ba Ta Mallakin Kowa Ba – Shugaban Matasa Ya Bayyana


Shugaban matasan jam’iyyar ADC na ƙaramar hukumar Zariya, Hon. Haruna Abdulkarim, ya bayyana cewa jam’iyyar ba mallakin wani mutum guda ba ce. Ya ce ba za su amince da duk wanda ya sauya sheka daga wata jam’iyya ya zo yana ƙoƙarin jagorantar su daga nesa ba.


ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta na Facebook a yau Laraba.Yana mai cewa su ne suka gina ADC tun daga tushe a Zariya. 

Ya tuna yadda ya tsaya takarar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna a cikin birnin Zariya  a 2023, yayin da Hon. Muhammad Kabir shi ma ya tsaya a Zariya Waje a wannan shekarar.

Haka kuma, ya ce jam’iyyar ta kuma gabatar da ɗan takara a zaɓen cike gurbi na baya-bayan nan. Ya ƙalubalanci masu shakka da su duba bayanai a ofishin INEC ko a shafukan yanar gizo domin tabbatar da hakan.

Bugu da ƙari, ya ce su ne suka shirya babban taron ƙasa na jam’iyyar ADC na shekarar 2022 a ABU Congo Conference. Ya ce wannan ya nuna irin rawar da suka taka wajen bunƙasa jam’iyyar.

A ƙarshe, Hon. Haruna Abdulkarim ya gargaɗi cewa ba za su bari masu cin gajiyar jam’iyyun APC, SDP da PDP su ƙwace musu jam’iyyar ba. Ya yi kira ga haɗin kai da bai wa kowace jam’iyya damar fafatawa cikin adalci.

Comments

Popular posts from this blog

ABUTH Zaria inducts 267 Health Information technicians, technologists

Usman Sulaiman emerges ASUP NBPZ Chairman unopposed, pledges inclusive leadership

MBY Declares Intention to Contest for Zaria Federal Constituency Seat in 2027