Kungiyoyin matasa a shiyya ta daya a jihar kaduna sun bukaci dawowar sanata kwari a karo na 2


Gamayyar kungiyoyin matasa a shiyya ta daya (Zone 1) a jihar Kaduna sun bayyana bukatar sake dawo da Sanata Suleiman Abdu Kwari domin ya sake wakiltar yankin a majalisar dattawan kasar nan karo na biyu. Kungiyoyin sun ce wannan kira ya biyo bayan nazari da tuntubar juna da suka gudanar kan halin da yankin ke ciki da kuma irin wakilcin da ya gabata.

Rahotanni sun nuna cewa kungiyoyin matasan sun cimma wannan matsaya ne bayan wata ganawar sirri ta musamman da suka gudanar a karamar hukumar Sabon Gari. Ganawar ta gudana karkashin jagorancin Abdulmajid Aliyu, inda aka tattauna batutuwa da suka shafi cigaban yankin da bukatar shugabanci nagari.

Taron ya samu wakilcin al’umma daga dukkanin kananan hukumomin da ke karkashin shiyya ta daya (Zone 1) a jihar Kaduna, lamarin da ya kara karfafa muhimmancin matsayar da aka cimma. 

Mahalarta taron sun bayyana ra’ayoyinsu tare da jaddada bukatar shugabanci mai nagarta da rikon amana.

A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Juma’a, sun bayyana cewa a tarihin shiyya ta daya ba a taba samun wakilci mai ma’ana, nagarta da inganci irin wanda Sanata Suleiman Abdu Kwari ya bayar ba. Sun kara da cewa ayyukansa sun taba fannoni da dama da suka hada da ilimi, ababen more rayuwa da tallafawa al’umma.

A karshe, gamayyar kungiyoyin matasan sun yi kira ga daukacin al’ummar yankin da su mara wannan yunkuri baya, tare da rokon Sanata Suleiman Abdu Kwari da ya amsa kiran al’umma domin ci gaba da yi musu hidima da kuma share musu hawaye.

Comments

Popular posts from this blog

ABUTH Zaria inducts 267 Health Information technicians, technologists

Usman Sulaiman emerges ASUP NBPZ Chairman unopposed, pledges inclusive leadership

MBY Declares Intention to Contest for Zaria Federal Constituency Seat in 2027