Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa reshen Jihar Kaduna, ya koka kan yadda ake hana ‘yan jarida damar shiga kotu wajen bin diddigin shari’ar tsohon gwamnan jihar.
Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa reshen Jihar Kaduna, Abdulgafar Alabelewe, ya koka kan yadda ake hana ‘yan jarida damar shiga kotu wajen bin diddigin shari’ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Ya ce tun lokacin da shari’ar ta fara, an rika hana ‘yan jarida shiga kotu, inda ake dogaro da bayanan lauyoyi kawai bayan kowane zaman shari’a. Ya bayyana hakan a matsayin abin damuwa ga ‘yancin aikin jarida.
Alabelewe ya ce hana kafafen yaɗa labarai shiga kotu na rage muhimmancin aikin jarida a batutuwan da suka shafi sha’anin ƙasa. Ya ce irin waɗannan shari’o’i na da matuƙar muhimmanci ga jama’a musamman na cin hanci ko tsaro.
Ya kuma ce wannan matsala ba ta Kaduna kaɗai ba ce, domin an sha samun irin haka a wasu lokuta, inda ake hana ‘yan jarida shiga ko kuma a takaita musu damar shiga kotu. Ya ƙara da cewa hakan na haifar da ruɗani a rahotanni.
A ƙarshe, ya yi gargadin cewa irin wannan mataki na iya jefa ‘yan jarida cikin haɗari da kuma rage sahihancin bayanai da ake watsawa ga jama’a.
Comments
Post a Comment